Buhari ya bada odar kuɓutar da ɗaliban Islamiyya 200 da aka sace a Tegina

Daga UMAR M. GOMBE

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya umarci fannin tsaron ƙasa da ya hanzarta ganowa tare da kuɓutar da ɗaliban Islamiyya su 200 da aka sace a Jihar Neja.

Shugaba Buhari ya bada odar hakan ne cikin wata sanarwa da mai magna da yawunsa, Malam Garba Shehu, ya fitar a Abuja a Litinin da ta gabata.

A cewar Shehu, Buhari ya yi tir da faruwar lamarin bayan da labari ya isa gare shi. Tare da yin kira ga ɗaukacin hukumomin da lamarin ya shafa da su gaggauta yin abin da ya kamata don kuɓutar da ɗaliban.

Haka nan, Buhari ya buƙaci hukumomin bada agaji da su duba sannan su tallafa wa iyalan yaran da aka yi garkuwa da su da gudunmawar da ta dace.

A Lahadin da ta gabata Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Neja ta tabbatar da sace yaran haɗa da wasu mazauna garin Tegina da ke yankin Ƙaramar Hukumar Rafi a jihar.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Adamu Usman, ya shaida wa manema labarai a Minna cewa, an sace ɗaliban ne a makarantar Islamiyya ta Salihu Tanko da misalin ƙarfe uku na rana a lokacin da ‘yan fashin daji suka kai wa garin hari a bisa babura.

Binciken Manhaja ya gano cewa an ga iyayen yaran da lamarin ya shafa sun yi cirko-cirko a harabar makaranta suna tsumayar yadda za a yi ‘ya’yan nasu su kuɓuta.