Buhari ya bai Gwamnan CBN izinin barin ƙasa gabanin rantsar da Tinubu

*DSS ta nuna rashin jin daɗinta kan bai wa Emefiele izinin ficewa daga ƙasa

Sahihan bayanai na nuni da cewa, Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya samu izinin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a kan ya tafi ƙaro ilimi a ƙetare.

A cewar Sahara Reporters, hakan zai bai wa Emefiele damar ficewa daga ƙasar kafin Buhari ya bar mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023.

Wanda hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake zargin Emefiele da aikata ba daidai ba da suka haɗa da cin hanci da rashawa da kuma ɗaure wa ta’addanci gindi.

Idan za a iya tunawa, Hukumar DSS ta zargi Emefiele da ɓarnata tattalin arziki, ƙarfafa wa ta’addanci da kuɗi da dai sauran laifuka masu nasaba da kassara tattalin arziki.

Haka nan, a baya ‘yan sandan ciki sun yi yunƙurin tsare Emefiele ɗin kan zarge-zargen da aka ɗora masa.

Jaridar Sahara Reporters ta rawaito cewar DSS ta nuna rashin jin daɗinta da yadda take ganin Gwamnan CBN na kakkauce wa shari’a.

“DSS ba ta yi na’am da izinin barin ƙasa da aka ce an bai wa Emefiele ba wanda hakan ke nufin zai fice daga ƙasa kafin 29 ga Mayu inda sabuwar gwamnati za ta shigo,” kamar yadda wata majiya ta bayyana a ranar Juma’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *