Buhari ya buƙaci sabon Sarkin Kagara ya zamo mai yi wa talakawansa hidima

Garba Gunna

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya taya Alhaji Ahmad Garba Gunna murna bisa naɗa shi da aka yi a matsayin sabon Sarkin Kagara da Gwamnan Neja Abubakar Sani Bello ya yi.

Kafin naɗin nasa, Garba Gunna shi ne shugaban hukumar tara haraji na jihar Neja.

Buhari ya yi kira ga sabon sarkin da ya yi amfani da sanin da yake da shi wajen yi wa talakawan masarautarsa hidima da kuma kawo wa masarautar cigaba.

Kazalika, Buhari ya buƙaci basaraken da ya yi amfani da matsayinsa wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’arsa, tare da jaddada cewa masarautu na da muhimmiyar rawar da suke takawa game da abin da ya shafi sha’anin tsaro.

Daga nan, Buhari ya yi fatan wa’adin mulkin sabon sarkin ya zama sila na samun tabbatacen tsaro da zaman lafiya da bunƙasa a yankin Kagara baki ɗayansa.

An naɗa Alhaji Garba Gunna a matsayin sabon sarkin Kagara ne biyo bayan rasuwar tsohon sarki Alhaji Salihu Tanko kwanan nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *