Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da dakatar da Kwamishinan Zaɓen Jihar Adamawa, Hudu Yunusa Ari, har zuwa lokacin da Sufeto Janar na ’Yan Sandan Nijeriya, Alƙali Baba Usman, zai kammala bincike a kan sa sakamakon sanar da sakamakon zaɓen Gwamnan Jihar Adamawa tun gabanin a kammala tattara sakamakon zaɓen da kuma kasancewar ba shi da hurumin aikata sanarwar, kamar yadda Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana.
Hakan ya na qunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai a Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Willy Bassey, ya fitar a jiya Alhamis.
Shugaba Buhari ya kuma bayar da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa tare da gurfanar da shi a gaban kuliya.
Har ila yau, Shugaban Ƙasar ya bayar da umarni ga Babban Sufeton ‘Yan Sanda da Darakta Janar na Hukumar Jami’an Farin Kaya (DSS) da kuma Babban Kwamandan Rundunar Tsaron Fararen Hula ta Nijeriya (Subil Difens) da su gudanar da bincike game da rawar da jami’ansu suka taka wajen bayar da taimako da gudanar da aika-aikar da ake zargin Barista Hudu Yunusa Ari ya aikata, idan har aka same shi da laifi a cikin badaƙalar.
Tun da fari dai Kwamishinan Zaɓen ya ayyana ‘yar takarar Jam’iyyar APC, Sanata Aishatu Dahiru Binani, a matsayin wadda ta lashe zaɓen Gwamnan Jihar Adamawa tun kafin kammala tattara sakamakon zaɓen.
Tuni dai Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa ( INEC) ta soke sanarwar Kwamishinan Zaɓen, sannan ta bayar da umarni da Jami’in Tattara Sakamakon Zaɓe a Jihar da ya kammala tattarawa da sanar da sakamakon, inda a ƙarshe ya sanar da Gwamnan Jihar mai ci, Umaru Fintiri, a matsayin wanda ya lashe zaɓen.