Buhari ya gargaɗi Obasanjo kan yi wa sha’anin zaɓe shisshigi

Daga WAKILINMU

Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo da kada ya haifar wa zaɓen 2023 da tasgaro da wasiƙar da ya rubuta na tada zaune tsaye da son-kai da tada hankali kan zaɓe.

A wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Talata, Ministan Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ce abin da tsohon Shugaban ƙasar ya yi ba komai ba ne illa ƙoƙarin haifar da cikas ga tsarin zaɓe da kuma yin magudin zaɓe da tada hankali.

Obasanjo ya ce babu nagarta a babban zaɓen ƙasar da aka yi ranar Asabar don haka ya ce dole ne a soke shi a yankunan da aka yi tashin hankali.

Ya buƙaci Shugaban Hukumar zaɓe ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu da ya ceci Nijeriya daga faɗawa haɗari.

Ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ya yi wa taken “Zaɓen Shugaban Nijeriya na 2023: Roƙon a yi taka tsan-tsan da kuma gyara.”

Obasanjo ya ce ba wani abin sirri ne, cewa an zargi wasu daga cikin ma’aikatan hukumar zaɓen da suka gudanar da aikin sun bayar da kai sakamakon aika alƙaluman zaɓen ba ta hanyar na’ura ba, abin da ya sa ake zargin wani sakamkon an ƙirƙire shi ne.