Buhari ya hana jiragen attajirai 91 tashi sakamakon gaza biyan haraji

Daga AMINA YUSUF ALI

A halin yanzu dai Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ta bayar da umarni ga hukumar Kwastan da su dakatar da wasu jirage 91 masu zaman kansu, mallakin wasu masu ƙumbar susa a ƙasar nan. A kan rashin biyan haraji sama da Naira biliyan 30. 

Idan za a iya tunawa, a kwanakin baya ranar 7 ga watan Yunin shekarar nan, hukumar kwastan ɗin ta fara aikin tantance jiragen saman masu zaman kansu inda ta nemi masu mallakin jirage masu zaman kansu da su garzayo ofishin hukumar domin tantancewa tare da satifiket ɗin jirgin saman, da lasisinsa da sauransu.

Hukumar Kwastam ta yi amfani da wannan dama don tabbatar da cewa sai jiragen sama ne kawai masu zaman kansu waɗanda suka haye waccan tantancewar ne kaɗai za su cigaba da aiwatar da harkokinsu. 

A sakamakon haka ne ya sa Kwanturolan hukumar hana fasa-kwaurin ta Kwastam, Kanal Hameed Ali mai ritaya, ya yi amfani da wancan Umarni na Shugaban ƙasa Buhari ya aike da wasiƙu daban-daban ga hukumomin kula da jiragen sama ta ƙasa, NCAA da hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama, da kuma hukumar da ke kula da filin tashin jirage a sararin samaniya, inda ya nemi hukumomin da su gaggauta dakatar da waɗancan jirage da suka gaza bin dokar biyan harajin. 

A cikin wasiƙar da aka aike wa hukumomin an bayyana cewa, Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta yi wannan yunƙuri ne a ƙoƙarinta na ƙara samun kuɗin shiga inda ta umarci mamallaka jiragen da su gaggauta biyan haƙƙin gwamnati da ke hannayensu.