Buhari ya hana jiragen sama shawagi a Zamfara

Daga FATUHU MUSTAPHA

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana dokar hana jiragen sama shawagi a Zamfara tare da haramta duka ayyukan haƙar ma’dinai a jihar.

Mai bai wa Buhari shawara kan harkokin tsaro, Major General Babagana Monguno (mai murabus) ne ya bayyana haka a ranar Talata a Abuja. Inda ya ce an ɗauki matakin haka ne domin kawar da matsalolin tsaron da ake fuskanta a jihar.

Monguno ya bayyana wa manema labarai haka ne jim kaɗan bayan kammala taron Majalisar Tsaro ta Ƙasa wanda ya gudana a Fadar Shugaban Ƙasa ƙarƙashin jagorancin Shugaba Buhari.

Wannan mataki na haramta wa jiragen sama shawagi a wani ɓangare, yanayi ne da sojoji kan mallaki ikon wani yanki wanda babu wani jirgin sama da zai gitta ta wannan wuri sai jiragen da aka amince musu kaɗai.

A cewar Munguno an buƙaci Hukumar Tsaro da Tattara Bayanan Sirri ta zauna da shirinta a kowane lokaci sannan kada ta bari ƙasa ta faɗa cikin hali mara kyau.

Tare da cewa, Shugaba Buhari ya bai wa sabbin shugabannin tsaro odar da su ƙwato duka yankunan da ke hannun ɓata-gari.