


Daga UMAR GARBA a Katsina
A yau Asabar ne ake gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi 34 na Jihar Katsina inda jam’iyyu biyar ke fafatawa.
Jam’iyyun sun haɗa da Accord, ADC, Booth, ADP da kuma jam’iyya mai mulki, wato APC.
Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na ɗaya daga cikin fitattun mutane da suka jefa ƙuri’arsu a zaɓen.
Buhari ya jefa ƙuri’ar ne a gundumarsa ta Sarkin Yara dake garin Daura inda ya samu rakiyar manyan ƴan siyasa a lokacin da ya isa rumfar zaɓe da misalin ƙarfe 11:10 na safe.

Haka ma Gwamnan jihar, Dikko Umar Raɗɗa da uwargidansa Hajiya Zulaihat sun isa rumfar zaɓe a unguwar Raɗɗa dake ƙaramar hukumar Charanchi cikin tsauraran matakan tsaro.
Mataimakin gwamnan jihar, Faruk Joɓe da tsofaffin gwamnonin Jihar, Ibrahim Shema da Aminu Bello Masari da wasu ministoci da sanatoci da suka fito daga jihar suma sun kaɗa ƙuri’unsu a rumfunan zaɓensu.
Da ya ke jawabi jim-kaɗan bayan kaɗa ƙuri’arsa, Gwamna Raɗɗa, ya yaba da yadda ɗimbin masu kaɗa ƙuri’ar suka fito, inda ya ce haƙiƙa wannan ya nuna cewa dimokuraɗiyya ta kafu a jihar.
Gwamnan ya kuma tabbatar wa masu zaɓen cewa za a ƙirga ƙuri’unsu bisa gaskiya da adalci.

Ya ƙara da cewa ƴan takarar APC ne ya ke fatan za su yi nasara duba da irin ayyukan da ya ke yi a jihar, tun daga shekarar 2023.
Tun da farko Blueprint Manhaja ta rawaito cewa manyan jam’iyyun adawa irinsu PDP da NNPP da wasu jam’iyyu 84 sun ƙaurace wa shiga zaɓen bisa zargin ba za a gudanar da zaɓen bisa adalci ba, kalaman zargin da shugaban hukumar zaɓen jihar, Lawal Alhassan Faskari ya musanta.