Buhari ya kama hanyar naɗa sabbin ministoci

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya miƙa wasu sunaye guda bakwai ga Majalisar Dattawa don tabbatar da su a matsayin ministoci.

Sunayen na ƙunshe ne cikin wasiƙar da Buharin ya aika wa Shugaban Majlaisar, Ahmad Lawan, inda shi kuma Lawan ɗin ya karanto wasiƙar yayin zaman majalisar a ranar Talata.

A cikin wasiƙar, Buhari ya bayyana cewa, buƙatar neman tabbatar da ministocin ta yi daidai da Sashe na 147 ƙaramin sashe na 2 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 wanda aka yi wa gyara.

Sunayen da lamarin ya shafa su ne: Henry Ikechukwu Ikoh (Abia), Umana Okon Umana (Akwa Ibom), Ekumankama Joseph Nkama (Ebonyi) da kuma Goodluck Nana Opiah (Imo).

Sai kuma Umar Ibrahim El-Yakub (Kano) da Ademola Adewole Adegoroye (Ondo) da kuma Odum Odi (Ribas).

Buhari na shirin naɗa sabbin ministocin ne don maye gurbin wasu daga cikin ministocinsa da suka yi murabus don shiga takara, irin su Amaechi da sauransu.