Buhari ya karɓi baƙuncin Bankole da Gbenga Daniel

Daga FATUHU MUSTAPHA

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya karɓi bakuncin tsohon Shugaban Majalisar Wakilai, Mr Dimeji Bankole da tsohonn Gwamnan Jihar Ogun, Mr Gbenga Daniel a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja bayan da suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.

Tawagar ta ziyarci Fadar Shugaban ƙasar ne ƙarƙashin jagoranci Shugaban Kwamitin Riƙo na APC kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni tare da Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi da kuma Gwamna Mohammed Badaru na Jigawa.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai jim kaɗan bayan kammala ganawarsu, Mai Mala Buni ya ce Shugaba Buhari ya yi matuƙar farin ciki da sauyin sheƙar da ƙusoshin siyasar suka yi.

Ya ce, “Mun zo ne domin gabatar da sabobbin mamabobi jam’iyyarmu ga Shugaban Ƙasa, wato Daniel da Bankole. Buhari ya yi murna da yadda aka samu jiga-jigan ‘yan siyasa irin waɗannan da suka amince su shigo jam’iyyarmu a daidai lokacin da ake yi wa sabbin mamabobi rajista, kuma wannan shi ne lokacin da ya dace su shigo cikinmu. Wannan lamari ya faranta wa Shugaban Ƙasa rai matuƙa.”

A nasa ɓangaren, tsohon Shugaban Majalisar Wakila ta Ƙasa Mr Dimeji Bankole, ya ce ya shiga APC ne domin ya bada tasa gudunmuwa ga ƙoƙarin da Shugaba Buhari ke yi wajen magance matsalolin ƙasa.

A cewarsa, “Akwai abubuwa da muke so mu magance su wanda duk wani mai tunani ya kamata ya bada tasa gudunmuwa a daidai wannan lokaci. Kama daga Barno zuwa Legas, Bayelsa zuwa Sakkwato. Waɗanan lokuta ne masu muhimmanci wanda bai kamata a bar mu baya ba.

“Yanzu ne lokacin da ya dace mu yi ɗamarar sannan mu bada gudunmawarmu ta yadda nan da shekara 10 ko 20 masu zuwa, ‘yan kasa za su buƙaci sanin waɗanda suka yi tsayin daka wajen magance matsalolin ƙasa. Haƙƙi ne da ya rataya a kan kowane ɗan ƙasa, amma abin da muka yi yau shi ne zai bayyana mu gobe.”

Shi ma tsohon Gwamanan jihar Ogun kuma Darakta Janar na kwamitin Yaƙin Neman Zaɓe na Alhaji Atiku Abubakar a 2019, Mr Gbenga Daniel, ya jaddada buƙatar mutane a daina kafewa a ce sai jam’iyya kaza wajen jagorancin ƙasa.

Ya ce, “Mun zaɓi shiga APC ne saboda akwai damarmaki da mutum zai bada gudunmawarsa. Gaskiyar al’amari shi ne, muna fama da matsalolin kiwon lafiya da tattalin arziki, wajibi ne mu taƙaita kwaɗayin yin takara sannan mu bada gudunmawarmu.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *