Buhari ya karɓi baƙuncin Guterres a fadarsa

Daga BASHIR ISAH

A ranar Laraba Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya karɓi baƙuncin Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Bayanai daga Fadar sun nuna Buhari ya yi ganawar sirri tare da baƙon nasa inda suka tattauna batutuwa da suka shafi Nijeriya, Afirka da sauransu.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa, Guterres ya zo ziyarar aiki ne na kwana biyu a Nijeriya, inda a ranar Talata ya ziyarci Maiduguri babban birnin Jihar Borno ya gana da waɗanda rikicin ta’addanci ya shafa da kuma mayaƙan Boko Harama da suka ajiye makaminsu.

Yayin ziyarar tasa, Guterres ya jagoranci dasa furanni domin tunawa da waɗanda suka rasu a harin bam da aka kai ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya da ke Abuja a 2011.

Wannan ita ce ziyarar farko da Guterres ya yi a Nijeriya tun bayan da ya zama Babban Sakataren MƊD.