Buhari ya karvi baƙuncin fitaccen ɗan kasuwa, Ummaru Shagalinku a Abuja

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Shahararren fitaccen ɗan kasuwaa Nijeriya, Alhaji (Dakta) Ummaru Shagalinku, mamallakin gidan abinin nan mai suna Shagalinku a fadin Arewa, ya kai ziyarar ban-girma da gaisuwar sallah ga Shugaban Ƙasa kuma Kwamandan Askarawan Nijeriya, Muhammad Buhari, a fadarsa dake babban birni tarayya Abuja radar 23 ga Afrilu, 2023.

Bayan gaisuwar sallah, Shugaba Buhari ya tattauna da ɗan kasuwar muhimman batutuwa, musamman akan fannin kasuwanci, inda bayan kammala ganawar nasu ne Alhaji Ummaru Shagalinku ya bayyana wa manema labarai farin cikinsa ciki har da Wakilin Blueprint Manhaja a ciki.

Alhaji Ummaru ya kuma taya al’umma Musulmai murnar kammala azumin watan Ramadan da shagulgulan sallah, inda ya yi addu’ar Allah ya amsa ibadunmu, ya sa mu na cikin ‘yantattun bayi. Haka nan ya yi fatan Allah ya zaunar da Nijeriya lafiya.

A ƙarshe ya yi kira ga al’ummar Nijeriya da su zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya kuma ya janyo hankalin matasa da su zama wakilai nagari a duk inda suka sami kansu.

Sai kuma babban ɗan kasuwar ya yi fatan alheri ga Sshugaban Buhari.

Ɗan kasuwar ya ce, za su manta da gudummawar da shugaban ya bayar ba a ɓangarori da dama, inda ya ce, Allah ya saka mashi da alheri.