Buhari ya koma Abuja bayan kammala zaɓen gwamnoni

Daga UMAR GARBA a Katsina

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya koma Abuja bayan kammala zaɓen gwamnoni da na majalisar jihohi da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata.

Mataimaki na musamman ga Shugaban Ƙasar kan kafafen yaɗa labarai na zamani, Bashir Ahmad ne ya bayyana haka a shafinsa na sada zumunta.

Yayin zaɓen, Shugaba Buhari ya kaɗa ƙuri’arsa ne a Ƙofar Baru, Sarkin Yara A, rumfa mai lamba 003 dake Daura, Jihar Katsina.

Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Dikko Umar Raɗɗa ne ya lashe zaɓen Gwamna a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *