Buhari ya miƙa ragamar buga kuɗin Nijeriya ga ɗan uwan matarsa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wani rahoto daga jaridun Nijeriya ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da naɗin Ahmed Halilu matsayin sabon manajan daraktan Nigerian Security Printing and Minting Company, NSPMC. 

Amintar shugaban ƙasan kan naɗin Halilu matsayin manajan daraktan kamfanin buga kuɗin na Nijeriya ya biyo bayan shawarar Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Godwin Emefiele. Wannan naɗin ya zo ne bayan watanni kaɗan da murabus ɗin Abbas Masanawa, tsohon manajan daraktan NSPMC. 

Sai dai, naɗin da aka yi wa Halilu zai aiki ne matsayin muƙaddashin manajan daraktan bayan shawara ta musamman da Godwin Emefiele, gwamnan babban bankin Nijeriya wanda a halin yanzu shi ne shugaban kwamitin NSPMC Plc. 

Ahmed Halilu dai yaya ne ga uwargidan Shugaban Ƙasa wanda yake da gogewar aƙalla shekaru ashirin a fannin aikin banki, inda ya samu gogewarsa a masana’antu kuɗi kamar African International Bank Limited, AIB da Zenith Bank. 

Karatunsa ne ya saka shi a sahun gaba na masana a ɓangaren aikin banki, inda yake da digirin farko a fannin noma da kiwo.

Yana da digiri na biyu a fannin kasuwanci da wani a fannin hulɗar ƙasashen ƙetare da diflomasiyya duk daga Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya. 

Halilu mamba ne a tsangayar gudanarwa ta NIM.