Buhari ya miƙa tutar jam’iyya ga gwamnonin da suka sauya sheƙa zuwa APC

A Litinin da ta gabata Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya karɓi baƙuncin gwamnonin Cross River da
Zamfara da suka sauya sheƙa zuwa APC kwanan nan a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja

Sun yi ziyarar ne ƙarƙashin jagorancin shugaban APC na ƙasa, Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe.

Yayin ziyarar, Buhari ya miƙa wa Gwamnan Cross River, Farfesa Ben Ayade da takwaransa na Zamfara, Bello Matawalle, tutar jam’iyyar APC a matsayin wani mataki na yi musu maraba da zuwa APC.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *