Buhari ya naɗa Adetifa a matsayin sabon shugaban Hukumar NCDC

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa Dr Ifedayo Morayo Adetifa a matsayin sabon shugaban Hukumar Yaƙi da Yaɗuwar Cututtuka ta Ƙasa (NCDC).

Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Garba Shehu, shi ne ya bayyana naɗin Adetifa a jiya Litinin.

Da wannan, ya tabbata Adetifa ya zama magajin Chikwe Ihekweazu wanda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta naɗa shi a muƙamin Mataimakin Darakta-Janar na hukumar.

Cikin wata wasiƙa da ya aika wa Ihekweazu, Shugaban WHO, Tedros Ghebreyesus, ya bayyana Ihekweazu a matsayin mataimakin shugaban sashen tattara bayanan gaggawa na hukumar.

Kazalika, wasiƙar ta nuna Ihekweazu sai  soma aiki a WHO daga ranar 1 ga Nuwamban 2021 a Berlin ta ƙarsar Jamus.

Tun a Agustan 2016 ne Shugaba Buhari ya naɗa Ihekweazu a matsayin shugaban NCDC.