Buhari ya naɗa Ilelah shugaban NBC

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya sauke Farfesa Armstrong Idachaba a matsayin shugaban Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin ta Ƙasa (NBC) sannan ya maiye gurbinsa da Balarabe Shehu Ilelah.

Kafin sauke shi, an bai wa Idachaba riƙon wannan muƙami tun Fabrairun 2020.

Ministan Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana naɗin da aka yi wa Ilelah a wata sanarwar manema labarai da ya fitar ran Juma’a. Tare da cewa, Ilelah zai riƙe NBC ne na tsawon shekara biyar.

Tun farko, gwamnati ta dakatar da Moddibo Kawu a matsayin shugaban NBC inda ta bai wa Farfesa riƙon matsayin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *