Daga IBRAHIM HAMISU
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da naɗin ɗan majalisar wakilai mai barin gado mai wakiltar Ƙaramar Hukumar birnin Kano, Sha’aban Sharaɗa a matsayin Babban Sakataren Zartarwa na sabuwar Hukumar Almajirai ta Ƙasa.
Mai magana da yawun shugaban Buhari mai barin gado Malam Garba Shehu ne ya tabbatar da hakan a daren Lahadi a Abuja.
A cewar Shehu, naɗin Sharaɗa ya biyo bayan amincewar da Shugaban Ƙasa ya yi ne na samar da hukumar kula da almajirai da ilmin yara ta kasa ta 2023.
Sharaɗa ya yi Digiri na farko a fannin jarida a Jami’ar Bayero ta Kano, sannan kuma ya yi Digiri na biyu a fannin harkokin kasuwanci daga Jami’ar Chichester, dake Birtaniya.