Buhari ya naɗa Yahaya a matsayin magajin Attahiru

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya naɗa Major General Farouk Yahaya a matsayin sabon Shugaban Rundunar Sojojin Nijeriya.

Kafin naɗin nasa, Major General Yahaya babban jami’i ne mai kula da ɓangare na 1 na rundunar sojojin Nijeriya, haka nan shi ne shugaban rundunar shirin Operation HADIN KAI mai yaƙi da ta’addanci a yankin Arewa-maso-gabas.

Cikin sanarwar da ya fitar a Alhamis, Daraktan riƙo na sashen labarun rundunar, Brigadier General Onyema Nwachuku, ya buƙaci kafafen yaɗa labarai da su yaɗa wannan bayani domin sanar da ‘yan ƙasa halin da ake ciki.

Da wannan naɗin, ya tabbata cewa Major General Farouk Yahaya ya zama magajin Ibrahim Attahiru wanda ya rasu tare da wasu jami’ai sakamakon haɗarin jirgin sama a Juma’ar da ta gabata a Kaduna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *