Buhari ya nemi amincewar Majalisar Tarayya don kinkimo bashin biliyan $4 da miliyan €710

Duk da ƙorafe-ƙorafen da ‘yan ƙasa ke yi game da yawan bashin da gwamnati ma ci ta ciyo, Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi Majalisar Dattawa da ta amince masa kan sake kinkimo bashin Dala biliyan 4 da Euro miliyan 710 daga ƙetare

Buƙatar Buhari na ƙunshe ne cikin wata wasiƙa da ya aika wa Shugaban Majalisar Dattatawa, wanda shugaban majalisar ya karanta ta a zauren majalisar a ranar Talata.

A cewar Buhari, za a biya bashin da ake shirin karɓowa ne ta hanyar samo wasu basussukan daga Bankin Duniya da Cibiyar French Development da Bankin EXIM da kuma IFAD.

Ya ci gaba da cewa, idan ska amince da karɓo wannan bashin, hakan zai taimaka wa gwamnati wajen aiwatar da wasu muhimman ayyuka a sassan ƙasa.

Wasiƙar ta nuna tun a watan Yunin 2021 Majalisar Zartarwa ta Ƙasa ta aminta da a aiwatar da wasu muhimman ayyuka a sassan ƙasa.

Haka ma majalisar ta da amince kan a kinkimo bashi daga Bankin Duniya da Cibiyar French Development da Bankin EXIM da kuma IFAD da ya kai $4,054,476,863 da Euro miliyan €710 don aiwatar da ayyukan.