Buhari ya nuna alhininsa kan rasuwar Jakande

Daga FATUHU MUSTAPHA

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya nuna alhininsa dangane da mutuwar tsohon gwamnan jihar Legas, Chief Lateef Jakande, wanda Allah Ya yi wa cikawa a Alhamis da ta gabata.

Sanarwar da ta fito ta hannun mai bai wa shugaban shawara kan sha’anin labarai da hulɗa da jama’a, Femi Adesina, Buhari ya ce marigayin ya yi rayuwa irin wadda al’umma ta amfana da ita.

Sanarwar ta bayyana Jakande a matsayin mutum wanda ƙasa da al’umma suka amfana da rayuwarsa, wanda za a daɗe ana tunawa da kyawawan ayyukan da ya gudanar.

Buhari ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin gami da ‘yan’uwa da abokan arziki da masu faɗa a ji na Legas da ma al’ummar jihar baki ɗaya.

A halin rayuwarsa, Jakande wanda tsohon ɗanjarida ne, ya yi gwamna a Jihar Legas daga 1979 zuwa 1983. Haka nan, ya riƙe muƙamin Ministan Ayyuka a zamanin mulkin marigayi Sani Abacha.

An haifi marigayin ne a ranar 23 ga Yulin 1929, a Legas inda ya bar duniya yana da shekara 91.