Buhari ya rantsar da Ariwoola a matsayin alƙalin alƙalan Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya rantsar da Mai Shari’a Olukayode Ariwoola a matsayin Alƙalin Alƙalan Nijeriya.

Shugaban ƙasar ya rantsar da Mai Shari’a Ariwoola a yau Larabar gabanin jagorantar Taron Majalisar Zartarwa a Fadar Gwamnatin Tarayya da ke Abuja.

Naɗin Ariwoola ya biyo bayan ajiye aikin da tsohon Alƙalin Alƙalai, Ibrahim Tanko Muhammad ya yi a watan Yuni, sakamakon rashin lafiya da ya yi ikirarin yana fama da ita.

A watan Yuni ne dai Buhari ya rantsar da Ariwoola a matsayin Alƙalin Alƙalan Nijeriya na riƙo, inda ya ci gaba da zama wannan mataki har zuwa lokacin da Majalisar Tarayya ta tantance shi a matsayin tabattacen alƙalin Alƙalan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *