Buhari ya rattaɓa hannu kan Dokar Kare Haƙƙin Mallaka

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya rattaɓa hannu kan Dokar Kare Haƙƙin Mallaka ta 2022 da kuma wani ƙudiri guda da Majalisar Tarayya ta zartar kwanan nan.

Rattaɓa hannun ya haɗa da Dokar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya na Medical Laboratory da ke Jos, ta 2023.

Babban Hadimin Shugaban Kan Harkokin Majalisar Wakilai, Hon. Nasiru Baballe Ila, shi ne ya bayyana haka cikin sanarwar da ya fitar ranar Alhamis.

Baballe ya ce Buhari ya sanya wa dokokin biyu hannu ne a ranar 17 ga Maris.

Ya ce Dokar Kare Haƙƙin Mallakar ta 2022 wadda ta maye gurbin takwararta ta Cap C28, na Kundin Dokokin Tarayyar Nijeriya, 2004 ta samar da tsari da kariya da sarrafa haƙƙin mallaka.

Ya ƙara da cewa, sanya wa dokar hannu ya nuna zimmar da gwamnatin Buhari ke da ita ta bunƙasa tattalin arzikin ƙasa don yin gogayya da na sauran ƙasashen duniya.

“Manufofin kafa samar da dokar kamar yadda Sashen na 1 ya nuna, shi ne don kare haƙƙin mallakar marubuta.

“Tabbatar musu da adalci gami da samun gwaggwaɓin sakamako da kuma ɗaukaka dangane da ƙoƙarinsu, bunƙasa Hukumar Kare Haƙƙin Mallaka…” da dai sauransu.