Buhari ya roƙi ASUU ta janye yajin aikinta

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya miƙa roƙonsa ga Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) a kan ta janye yajin aikin da take yi sannan ta rungumi sulhu tsakaninta da Gwmanatin Tarayya.

Haka nan, Buhari ya buƙaci ɗaliban da lamarin ya shafa su ƙara haƙuri da lamarin Gwamnatin Tarayya, kana ya hore su da kar su saka kansu cikin dukkan wani hali da ka iya zama barazana ga zaman lafiyar ƙasa.

Buhari ya yi wannan roƙon da kiran ne a wajen taron karramawa na ƙasa da ya gudana a Babban Zauren Taro na Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Alhamis.

Idan dai ba a manta ba, kwanan nan ASUU ta tsawaita wa’adin yajin aikin da take yi da makonni 12 biyo bayan gazawar Gwamnatin Tarayya wajen cin ma buƙatunta.

Kawo yanzu, ɗaliban jami’o’i da ma iyayensu na ci gaba da nuna damuwarsu a kan yajin aikin ASUU tare da fatan ganin an samu daidaito tsakanin Gwamnati da ASUU domin kawo ƙarshen yajin aikin.

Kawo yanzu, ɗaliban jami’o’i mallakar Gwamnati na ci gaba da nuna damuwarsu a kan matsalar yajin aikin, tare da fatan ganin an samu daidaito a tsakanin ɓangarorin biyu domin kawo ƙarshen zaman gidan da suke yi.