Buhari ya sake naɗa Bashir Ahmad hadiminsa

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa Bashir Ahmad matsayin Hadimi na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Sadarwa na Zamani.

Sanarwar naɗin na ƙunshe ne cikin wasiƙar da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya aikawa Bashir ɗin mai ɗauke da kwanan watan 20 ga Yulin 2022.

Kafin wannan lokaci, Bashir Ahmad shi ne hadimin Shugaba Buhari kan sabbin kafafen yaɗa labari inda ya ajiye muƙamisan don yi takarar ɗan Majalisar Wakilai.

Cikin wasiƙar da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya gani, sabon muƙamin da Buhari ya bai wa Bashir zai fara aiki ne daga ranar 19 ga watan Yulin bana.

Idan dai ba a manta ba, gabanin zaɓen fitar da gwanayen takara ne Bashir Ahmad ya yi murabus daga muƙaminsa domin neman takarar ɗan Majalisar Wakilai na ƙananan hukumomin Gaya da Ajingi da Albasu da ke Jihar Kano.

Wanda ya yi daidai da umarnin da Buhari ya bai wa duk hadimansa na ajiye muƙamansu gabanin neman takarar wata kujerar siyasa.

Sai dai Bashir bai yi nasara ba, inda ya sha kaye a zaɓen fidda gwanin takarar, yana mai watsi da sakamakon zaɓen, wanda ya ce cike yake da ruɗani sakamakon rikicin da ya ce ya ɓarke a wurin zaɓen.