Buhari ya tsige muƙaddashin Akanta-Janar, Anamekwe saboda rashawa

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhmamadu Buhari ya tsige muƙaddashin Akanta-Janar na Ƙasa Chukwuyere N. Anamekwe.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, tuni aka maye gurbin Anamekwe da Mr. Okolieaboh Ezeoke Sylvis, tsohon Darakta na Asusun Bai-ɗaya (TSA), a matsayin mai riƙo.

Bayanai sun ce an tsige Anamekwe ne saboda dalilai masu nasaba da rasahawa, inda aka nuna cewa da ma dai Hukumar Yaƙi da Cin-hanci (EFCC) tana bincike a kansa saboda zargin rashawa.

An kuma ce, gwamanti ta nuna rashin gamsuwarta da kalaman da aka ce Anamekwe din ya yi cewa da bashi gwamnati ta biya albashin ma’aikata a watan Yuni.

An naɗa Anamekwe muƙaddashin Akanta-Janar na Ƙasa ne a ranar 22 ga Mayun da ya gabata biyo bayan dakatar da Ahmed Idris da aka yi kan zargin rashawa da kuma karkatar da kudin gwamnati da ya kai Naira biliyan 80.

Rahotanni sun ce, Gwamnatin Tarayya ta soma binciken wanda ya fi dacewa ta naɗa a matsayin sabon Akanta-Janar ɗin don ci gaba da gudanar harkokin ofishin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *