Buhari ya umarci Buni ya jagoranci taron APC bisa sharuɗɗa

Daga SANI AHMAD GIWA

Wasu rahotanni sun yi nuni da cewa gwamnan Jihar Yobe, kuma Shugaban Kwamitin Riƙon Ƙwaryar Jam’iyyar APC, Mai Mala Buni shi zai jagoranci gudanar da babban taron ƙasa da jam’iyyar ta tsayar a ranar 26 ga Maris, 2022.

Jaridar Punch ta jiyo cewa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya umarci Buni ɗin da ya jagoranci taron, amma ya yi masa kashedin cewa ba za a ƙara ɗage ranar yin babban taron jam’iyar na ƙasa ba.

Majiyoyi sun shaida wa Punch cewa Buhari ya ɗauki wannan matakin ne bayan ganawa da ya yi da wasu jiga-jigan jam’iyar a Landan.

Daga cikin Waɗanda suka bai wa Buharin shawarar ɗaukar wannan matakin akwai Antoni-Janar kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, wanda ya nuna wa shugaban ƙasar illar da za a iya samu ta ɓangaren shari’a.

Haka-zalika an jiyo cewa, bayan da a yanzu shugaban ƙasar ya nuna ba shi da wani ɗan takara a zaɓen shugaban jam’iyyar na dindindin, yanzu gurbin ya zamto a buɗe, inda kowa zai iya nema.

Hakan kuma, inji majiyoyi, ya nuna rashin tabbas a kan rabon muƙamai na shiyya-shiyya da jam’iyyar ta fitar a makon da ya gabata.

Haka kuma a ganawar ta birnin Landan, Buhari ya musanta bada umarnin cire Buni da kuma maye gurbinsa da Gwamna Abubakar Sani Bello kamar yadda Gwamna Nasir El-Rufai ya faɗa.