Buhari ya yi wa ‘yan Nijeriya ‘Barka Da Sallah’

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya miƙa saƙon barka da sallah ga ɗaukacin al’ummar musulmin Nijeriya da ma duniya baki ɗaya.

Buhari ya miƙa saƙon nasa ne ta hannun mai magana da yawunsa, Garba Shehu, yana mai cewa bayan kammala azumin bana ana da dukkan wata dama na maraba da bikin sallah.

Haka nan, Shugaban ya bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin “yaƙin da ake yi da ɓatagarin da suka fake da Musulunci suna cutar da jama’a ya kusa zuwa ƙarshe.”

Ya ce, “Yaƙi ne mai wahala wanda ya ɗauki tsawon lokaci, kuma a ƙarshe mun soma ganin nasara. An karya lagon Boko Haram.”

Sanarwar ta nuna irin nasarorin da gwamnati ta samu kawo yanzu wajen yaƙi da Boko Haram/ISWAP da ‘yan fashin daji a sassan ƙasa da kuma IPOB da ke Kudu haɗe da yaƙi da harkokin miyagun ƙwayoyi.