Buhari ya zaɓi sabbin shugabannin hukumar kamfanin NNPC

Daga AMINA YUSUF ALI

Shugaba Buhari ya zaɓi sababbin shugabannin hukumar kamfanin NNPC. Shugaban ƙasar Nijeriya, Muhammadu ya yi sabbin naɗe-naɗen muƙamai a sabon kamfanin NNPC.

Shugaban ya yi wannan naɗi ne da amfani da damar ikon da sashe na 59(2) na sabuwar dokar man fetur a kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar (2021) ya ba shi.

Kakakin Fadar Shugaban ƙasar, Mista Femi Adeshina shi ya tabbatar da wannnan labari ranar Larabar da ta wuce a Abuja.

A cewar sa, an naɗa wasu muƙamai kamar haka: Shugabar Kwamitin ita ce Sanata Margret Chuba Okadigbo, sai Mele Kolo Kyari, a matsayin Babban Jami’in zartaswa, sannan Umar I. Ajiya a matsayin Babban jami’in harkokin kuɗi.

Sauran mambobin sun haɗa da Dakta Tajudeen Umar (Arewa maso- Gabas), Mrs Lami Ahmed (Arewa ta tsakiya), sai Malam Mohammed Lawal (Arewa maso Yamma), sai Henry Obih (Kudu maso Arewa), Barrister Constance Harry Marshal (kudu maso kudu), Sai kuma Chief Pius Akinyelure(kudu maso Yamma).

Kuma rahotanni sun bayyana cewa, waɗannan zaɓaɓɓun mutane za su fara aiki ne daga ranar da NNPC ɗin zai fara cin gashin kansa.

Sannan kuma an zaɓi kwamishinonin zartarwar da za su shugabanci ɓangaren nemowa da haƙar man fetur ɗin.

Wato su ne, Dakta Nuhu Habib (daga jihar Kano), shi ne kwamishinan zartarwa na samarwa da bunƙasawa, sai Dakta Kelechi Onyekachi Ofoegbu (daga jihar Imo), sai Tonlagha Roland John (daga jihar Delta.) Da sauransu.

Sai dai duk da naɗe-naɗen nan na sabbabin mambobin da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi, bai canza shugaban na NNPC ba wato Abba Kyari. Har yanzu shi ne dai shugaba. Wato babban jami’in zartarwa a kamfanin na NNPC.

Waɗannan naɗe-naɗe sun biyo bayan tabbatar da NNPC a matsayin hukuma mai zaman kanta

Idan za a iya tunawa, a ƙarshen watan Satumbar Shekarar da ta gabata ne dai shugaba Buhari ya rubuta wasiqa ya aike wa da majalisar dattijai inda ya nemi a yi garambawul da kwaskwarima ga wasu dokokin masana’antar man fetur a cikin kundin tsarin mulkin ƙasar nan.

Abubuwan da Shugaban ya nemi a yi wa kwaskarima a dokar man fetur ɗin su ne, damar zaɓen mambobin kwamitin da ba na zartarwa ba, cire ma’aikatun man fetur da na kuɗi daga cikin mambobin kwamitin man fetur ɗin da kuma zaɓen daraktocin zartarwa.