Buhari ya zaɓi tsoffin hafsoshi a matsayin jakadu

Daga WAKILIN MU

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya miƙa sunayen tsoffin hafsoshin tsaron da suka yi murabus kwanan nan, ga Majalisar Dattawa domin amincewa da naɗa su a matsayin jakadu.

A cikin wasiƙar da Buhari ya aika wa Sugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan, Buhari ya ce, “Bisa la’akari da Kundin Tsarin Mulki sashe na 171 (1) da sashe na (2) (c) da ƙaramin sashe na (4) na Kundin Tsarin Mulki na 1999 na Tarayyar Nijeriya wanda aka yi wa gyaran fuska, ina mai gabatar da waɗannan sunaye guda 5 don neman amincewar Majalisar Dattawa kan yi musu naɗin Jakadu.”

Waɗanda lamarin ya shafa su ne: Gen Abayomi G. Olonisakin (mai murabus), da Lt Gen Tukur Y. Buratai (mai murabus), da Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai murabus), da Air Marshal Sadique Abubakar (mai murabus) sai kuma Air Vice Marshal Mohammed S. Usman (mai murabus).