Buhari ya ziyarci Saudiyya

A ziyarsa ya zuwa ƙasar Saudiyya, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya kai ziyara birnin Madina inda ya gabatar da ibadar da ta sawaƙa gare shi tare da tawagarsa inda suka yi addu’ar zaman lafiya ga Nijeriya da ma duniya baki ɗaya.

Tun farko bayan da ya isa babban filin jirgin sama na Yarima Muhammad Abdulaziz Airport a Madina, Mataimakin Gwamnan yankin, Yarima Sa’ud Al-Faisal ne ya tarbi Buhari inda suka kasance tare a Masallacin Annabi Muhammad, wuri na biyu mafi tsarki baya ga Masallacin Harami.

Shugaba Buhari da tawagarsa sun gabatar da ibada tare da yi wa Nijeriya da al’ummarta fatan alheri da lumana mai ɗorewa.

Ana sa ran ya zuwa yamma Shugaba Buhari zai tafi birnin Makka domin gabatar da Umurah.