Buhari zai rattaɓa hannu kan sabuwar dokar zaɓe, inji mashawarcinsa

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

A cikin taraddadin ƙila-wa-ƙala ko Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ba zai rattaɓa hannu akan dokar zaɓe da aka yi wa kwaskwarima ba cikin wa’adin kwanaki 30 na yin hakan, mai ba shi shawarwari a kan lamuran Majalisar Dattawa, Sanata Babajide Omoworare ya bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin cewar, Shugaba Buhari zai rattaɓa hannu akan dokar ta zaɓe.

Hadimin na Shugaban Ƙasa ya bayar da wannan tabbaci ne yayin wata tattaunawar jin ra’ayi da Cibiyar Lamuran Majalisa da Nazarin Siyasa ta shirya a birnin tarayya ta Abuja a satin da ya gabata.

Tattaunawar ta neman cimma manufa, ta alaƙa ne kacokan akan ‘Dokar Zaɓe ta Shekarar 2021 da Zumuɗin Sanya Hannun Shugaban Ƙasa: Bisa Majivantan Lamura’, Omoworare ya bayyana cewar, Shugaba Buhari yana tuntuɓar wasu madafun mulki kafin ya rattaɓa hannu akan dokar.

Dangane da tafiyar lokaci, Omoworare ya ce Ubangidan sa yana sane da sashe na 58 na kundin tsarin mulkin ƙasa na shekarar 1999 gyararre, wanda ya tanadi wa’adin kwanaki 30 na sanya hannu, yana bayar da tabbacin shugaba zai yi aiki da wancan tanadi ba tare da tangarɗa ba.

“Shugaban Ƙasa yana zumuɗin ya sanya hannu a kan dokar, amma yana tuntuɓa, kuma zai rattaɓa hannun cikin wa’adin yin hakan na kwanaki talatin.

Omoworare ya ce, “ba zan ari bakin sa na ci masa albasa ba. Komai zai biyo bayan tuntuɓa da yake yi ne, walau ya sanya hannu ko akasin haka, amma muna sane da cewar, muna cikin ƙalubalen lokaci.”

Shi ma da yake yin furuci akan batun, tsohon shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa mai cin gashin kan ta (INEC), Farfesa Attahiru Jega ya ce buƙatar kyakkyawar doka wacce za ta inganta lamuran zaɓe.

Jega ya kuma yi nuni da ɓaraka a cikin dokar ta zaɓe, musamman na tanade-tanaden da aka yi dangane da kuɗaɗen da ɗan takarar shugaban ƙasa zai kashe wajen yaƙin neman zaɓe.

Ya ce “akwai kyawawan ƙa’idoji na asali na tafiyar da lamuran siyasa. A ce ɗan takarar shugabancin ƙasa yana kashe zunzurutun kuɗaɗe Naira biliyan biyar, kuma ɗan takarar neman gwamna yana kashe Naira biliyan guda kan neman zaɓen sa, ya munana dokar.

“A nawa ra’ayin, lamari ɗaya ne tak a cikin kyawawan batutuwa mai kyau a cikin dokar. Walau a yi zaven ɗan takara ta hanyar ‘yar tinƙe, ko kuma ta hanyar fahimtar juna, bai haifar da komai ba matuƙar babu dimukuraɗiyya a cikin tsarin jam’iyyu.

“Idan babu dimukuraɗiyya a cikin tsare-tsaren jam’iyya, walau a yi zaven ɗan takara ta hanyar ‘yar tinƙe ko ta hanyar fahimtar juna, za su murɗe shirin, kuma sakamakon ba zai kasance karɓaɓɓe wa jama’a ba,” inji Jega.