Bunƙasa harshen uwa wata dama ce ta samun ci gaba da haɗin kan al’umma

Daga FA’IZA MUSTAPHA

Harshe ko yare, wata alama ce ta mutane daban-daban dake akwai a duniya. Shi ya sa Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware wata rana guda, ta 21 ga watan Fabrairun kowacce shekara, a matsayin ta tunawa da muhimmancin harshen uwa ga ci gaban duniya da al’adu da cudanya tsakanin al’ummun daban-daban.

Ban da haka, a ganina, karewa da kyautata amfani da harshen asali na wata ƙasa ko al’umma, na bada gagarumar taimako ga ci gaban al’umman. Misali, amfani da harshen uwa wajen koyarwa da gudanar da harkokin ƙasa, ba ƙaramin taimakawa ƙasashe masu tasowa zai yi ba wajen rainon al’umma da ciyar da su gaba. Nazarce-nazarce ma sun nuna cewa, dalibai sun fi fahimtar koyarwa cikin harshensu na asali maimakon harshen aro. A yanzu, musammam a ƙasashe masu tasowa, an fi mayar da hankali wajen koyon harsunan ƙasashen yammacin duniya musammam harshen Ingilishi maimakon harshen asali na yanki ko al’umma.

Zamana a ƙasar Sin, ya ƙara fahimtar da ni irin ɗimbin ci gaban da ƙasar ta samu, ba zai rasa nasaba da amfani da harshen Sinanci wajen gudanar da harkokin ƙasa da koyarwa da duk wani abu da ya shafi al’umma ba. Haka kuma, ya taka muhimmiyar rawa wajen kawo haɗin kai a tsakanin al’ummarta. Duk da cewa akwai tarin ƙabilu daban-daban a ƙasar Sin, harshen Sinanci, shi ne harshen da daukacin al’ummar ƙasar ke amfani da ita a hukumance.

A tunanina, wannan kaɗai misali ne da ya kamata a ce ƙasashenmu na Afrika sun yi koyi da shi, idan suna son samun ci gaba. Koyon wasu harsunan, shi ma abu ne mai muhimmanci, amma kuma bai kamata garin yin hakan, a manta da harshen asali ba. Ban da haka, koyarwar cikin harshen uwa zai rage kuɗin da ake kashewa wajen samar da ilimi, haka kuma zai tabbatar da daidaito a wannan fannin, tsakanin yaran da suka fito daga iyalai masu hali da waɗanda ba su da hali.

Idan muka yi duba kan manyan ƙasashen duniya, dukkansu na amfani ne da harsunansu na asali a matsayin babban harshen ƙasa, amma galibin ƙasashe masu tasowa, na amfani ne da harsunan ƙasashen da suka raine su.

A gaskiya, akwai buƙatar gwamnatoci su yi duba a kan wannan ɓangaren a matsayin wata hanya ta neman ci gaban al’umma da hadin kai da uwa uba tabbatar da ilimin zuri’a masu tasowa. Kamar yadda na ce, mayar da hankali kan harshen uwa bai zama watsi da sauran manyan harsunan ƙasashen waje ba. Sai dai, kamata ya yi harshen uwa ya zama a kan gaba. Kamar a ƙasar Sin, sai da kowanne dan ƙasa ya iya harshen Sinanci kafin koyon wasu harsunan waje. Duk inda ka je a duniya, za ka tarar Basine ya iya harshensa kuma zai iya mu’amala da kowanne Basine daga kowanne ɓangare na ƙasar Sin. Wannan ma na ɗaya daga cikin dalilan da suka sanya ƙasar ke kiyaye dadaddun al’adunta na gargajiya da aka gada daga kaka da kakanni, haka kuma yara da manya duk sun san tarihin waɗannan al’adu.