Buni da Badaru sun jagoranci zaman sulhu tsakanin ɓangaren Ganduje da Shekarau

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Yobe kuma shugaban kwamitin riƙo na jam’iyyar APC, Alhaji Mai Mala Buni, tare da takwaransa na Jihar Jigawa, Alhaji Abubakar Badaru, da sauran masu ruwa da tsaki sun gana da jagororin jam’iyyar APC na Jihar Kano.

Buni ne ya kira taron, wanda aka gudanar a Abuja ranar Talata, domin sasanta ɓangarorin jam’iyyar biyu a Kano, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abdullahi Ganduje da Sanata Ibrahim Shekarau.

Wasu majiyoyi sun shaida wa Daily Nigerian cewa, shugabannin jam’iyyar APC sun nuna damuwarsu kan rigingimun da suka dabaibaye jam’iyyar a Kano.

Ɗaya daga cikin mahalarta taron wanda ya zanta da Daily Nigerian bisa sharaɗin sakaya sunansa, ya ce jam’iyyar ta sha alwashin yin iya ƙoƙarinta na ganin ta kauce wa sake afkuwar irin abinda ya faru a jam’iyyar APC na Zamfara a Kano.

Dangane da shari’ar da ake yi a kotun ɗaukaka ƙara kuwa, shugabannin jam’iyyar sun nuna rashin jin daɗinsu kan yadda rikicin har ya kai ga kotu.

Ya ƙara da cewa shugabannin jam’iyyar sun kaucewa tattaunawa a kan shari’ar da ake tafkawa a kotu, inda suka ce ko mene ne sakamakon shari’ar, kowane ɓangare na buƙatar juna don samun nasara a zaɓe.

A wata sanarwa da kakakin gwamnan Yobe, Mamman Mohammed ya fitar, ya ce manufar taron ita ce a sulhunta shugabannin APC a Kano.

“A ƙarshen taron, mahalarta taron sun taya juna murna tare da nuna gamsuwa da sakamakon taron.

“Taron da aka yi a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Buni na daga cikin matakan da jam’iyyar ta ɗauka na sasanta ‘ya’yan da ba su ji ba gani kafin babban taron ƙasa da ke tafe.

“Kwamitin Buni ya ƙuduri aniyar warware rigingimun da ke tafe don tunkarar taron tare da haɗin kai,” inji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *