Buni ya lashe zaɓen gwamnan jihar Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Damaturu

Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta Ƙasa (INEC) ta ayyana Gwamna Mai Mala Buni na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen Gwamna a jihar Yobe.

Kwamishinan Hukumar INEC na jihar Yobe, Alhaji Ibrahim Abdullahi shi ne ya sanar da hakan a cibiyar tattara sakamakon zaɓen dake Damaturu, da daren nan.

Ya ce Gwamna Buni na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 317,113, fiye da na abokin takararsa daga jam’iyyar PDP, Hon. Shariff Abdullahi, mai adadin ƙuri’u 104,259, wanda hakan ya tabbatar da Buni a matsayin wanda ya samu nasara a zaɓen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *