Buratai ya kaddamar da manyan makaman atilare

Babban hafsan rundunar sojojin kasa na Nigeria, laftana janar Tukur Burtai ya kaddamar da manyan makaman atilare da kuma makarantar horar da dabarun yaki a Kachiya jihar Kaduna. Ya ce za a yi amfani da makaman ne a Arewa maso gabashin kasar nan ne, inda yan ta’adda su ka yi katutu.

Gwamnatin tarayya dai ce ta samar da makaman, kuma makamai ne na zamani wanda aka boye bayanan sanfuran su saboda tsaro.

A yayin da yake bayani ga manema labarai, mai magana da yawun rundunar sojin, kanal Sagir Musa ya ce, babban hafsan ya ziyarci makarantar ne da nufin ya tabbatar da ingancin makaman.

“Babban abinda hafsan ya sa a gaba shi ne samar da kayan aiki da kuma kyakkyawan yanayin aiki ga jami’an sojin kasar nan. A saboda haka ne Babban Hafsan ya qaddamar da wannan makaranta” Inji Kanal Sagir

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*