Burundi da Sin sun ƙulla yarjejeniyar zamanintar da babban filin jirgin saman Burundi

CRI HAUSA

A ranar Asabar, ƙasashen Burundi da Sin sun sanya hannu kan yarjejeniyar aikin faɗaɗawa da zamanintar da filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na Melchior Ndadaye, dake Bujumbura, babban birnin ƙasar Burundi.

An gudanar da bikin sanya hannu kan yarjejeniyar ne a ma’aikatar harkokin wajen Burundi, wanda ministan harkokin waje da bunƙasa haɗin gwiwa na ƙasar Burundi, Albert Shingiro, da jakadiyar ƙasar Sin a ƙasar Burundi, Zhao Jiangping suka jagoranta.

Zhao ta ce, aikin ya haɗa da ɓangarori uku, wato gyaran titinan jirgin sama, da wajen taruwar jiragen, da gina cibiyar sadarwa domin kula da tashi da saukar jirage, da ginin tafiyar da harkoki, da kuma samar da kayayyaki a fannonin ayyukan kula da sufurin jiragen sama, aikin sadarwa da hasashen yanayi.

Jakadiyar ta ƙara da cewa, wannan aiki ya ƙara bayyana ingantacciyar hulɗar ‘yan uwantaka dake tsakanin ƙasashen Sin da Burundi. Ta ce abokantakar dake tsakanin ƙasashen 2 ta kasance ta amincewar juna ce, da nuna wa juna goyon baya, da kuma samun moriyar juna.

A nasa ɓangaren, ministan harkokin wajen Burundin Shingiro ya ce, wannan wani muhimmin aiki ne da zai kara kyautata hulɗar dake tsakanin ƙasashen biyu.

Fassarawa: Ahmad

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *