Ƙungiyoyin fararen hula sun koka da matakin da gwamnatin Burundi ta ɗauka na ficewa daga zauren zaman nazartar kundinta na take haƙƙoƙin bil’adama da Majalisar Ɗinkin Duniya ke jagoranta.
Wannan ɗabi’ar da Burundi ta nuna ta jefa fargaba a zukatan ƙungiyoyin fararen hula da suka nuna damuwa kan yadda ƙasashen duniya ke bijire wa Majalisar Ɗinkin Duniya.
Lokaci zuwa lokaci, Majalisar Ɗinkin Duniya na gudanar da nazari kan yadda gwamnatocin ƙasashe ke mutunta dokokin kare haƙƙin bil’adama.
Sai dai a wani yanayi na ba-zata, tawagar wakilai 15 ta Burundi ta fice daga zaman da ta yi tare da Kwamitin Kare Haƙƙin Bil’adama na Majalisar Ɗinkin Duniya a ranar Litinin da ta gabata a birnin Geneva saboda abin da ta kira wasu miyagu da ke gabatar da kansu a matsayin mambobin ƙungiyoyin fareren hula.
Wannan ɗabi’ar da Burundi ta nuna, na zuwa ne bayan makamanciyarta da Nicaragua ta yi, wadda ta ki amincewa a yi zama da ita domin nazartar wata azabtarwa da ake zargin ta da aikatawa.
Kazalika ita ma Ƙasar Rasha sau biyu tana ƙaurace wa irin wannan zama tare da Majalisar Ɗinkin Duniya a bara na nazartar wasu daga cikin ayyukanta da ake ganin laifi ne.
Majalisar Ɗinkin Duniyar ta nuna damuwa kan yadda ƙasashen duniya ke bijire mata.