Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Sergio Busquets ya tabbatar da zai bar Barcelona a ƙarshen kakar nan, bayan shekara 18 yana buga wa ƙungiyar wasa.
Tsohon ɗan ƙwallon tawagar Sifaniya, mai taka leda daga tsakiya ya yi wa Barca karawa 718 – shi ne na uku a yawan buga wasa a ƙungiyar.
Ɗan ƙwallon ya lashe kyautuka da yawa a Barca ciki har da ɗaukar La Liga takwas da Copa del Rey bakwai da Spanish Super Cup bakwai da Champions League uku.
Busquets ya koma Barca a 2005 a matakin matashin ɗan awallo daga nan har ya koma babbar ƙungiyar, inda ya fara wasa ƙarƙashin Pep Guardiola a 2008 a gasar La Liga a karawa da Racing Santander.
Ɗan ƙwallon wanda ya lashe European Super Cups uku a Barca da Fifa Club World Cups uku zai ɗauki La Liga na tara a kakar nan.
Ƙungiyar da Xavi ke jan ragama tana matakin farko a kan teburin La Liga da tazarar maki 13, kuma saura wasanni biyar a kammala kakar bana.
A kaka 15 da ya yi yana buga wa babbar ƙungiyar Barcelona ya ci qwallo 18 ya kuma bayar da 40 aka zura a raga.
Busquets ya yi ritaya daga buga wa tawagar Sifaniyar tamaula a cikin watan Disamba, bayan da ya lashe kofin duniya a 2010 da European Cup a 2012.