CAF ta ɗage gasar Africa Nations Championship zuwa Agusta 2025

Daga USMAN KAROFI

Hukumar CAF ta sanar da ɗage gasar TotalEnergies CAF African Nations Championship (CHAN) 2024 zuwa Agusta 2025.

CAF ta bayyana cewa an ɗage gasar ne domin samar da ƙarin lokaci don tabbatar da cewa kayan aiki da wuraren da za a yi gasar sun kai matakin da ya dace don gudanar da gasar cikin nasara.

A yayin haka, hukumar za ta gudanar da zaɓen rukunin gasar TotalEnergies CAF CHAN a Nairobi, ranar Laraba, 15 ga Janairu, 2025.