Caleb Mutfwang na jam’iyyar PDP ya lashe zaɓen gwamna a jihar Filato

Daga AMINA YUSUF ALI

Hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana Caleb Mutfwang, ɗan takarar jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna na jihar Filato.

Wannan sanarwa ta fito ne daga Baturen zaɓe na INEC mai suna Musa Yusuf, bayan kammala qirga ƙuri’un dukka jam’iyyun da suka tsaya takara a zaɓen, wanda ya nuna Mutfwang shi ne da mafi rinjayen quri’u. Mutfwang ya lallasa ɗan takarar jam’iyyar APC, Nentawe Yilwatda.

Idan ba a manta ba, da ma ɗan takarar gwamnan na jam’iyyar PDP rahotanni da ma tuni sun nuna shi ke kan gaba wajen yawan ƙuri’un tun ƙarfe 11 na safiyar yau Litinin da INEC ta ɗora a kan cigaba da tattara sakamakon zaɓuɓɓukan daga faɗin ƙananan hukumomi 17 da suke a jihar.