CAN ta buƙaci ’yan siyasar da suka yi nasara su rungumi kowa

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

A yanzu da aka kammala duka zaɓukan gama-gari na 2023, an yi kira na musamman ga ’yan siyasa a dukka matakai a jihar Nasarawa da ƙasa baki ɗaya su tabbatar sun rungumi aƙidar zaman lafiya da haɗa kawunan al’umma maimakon ta da zaune tsaye da sauran su.

Shugaban Ƙungiyar Mabiya Addinin Kirista ta Ƙasa (CAN), reshin Jihar Nasarawa Dokta Sunday Emmah ne ya yi wannan kira a lokacin da yake tattauna da wakilinmu a gidan sa dake Lafiya fadar gwamnatin jihar a ƙarshen makon da ya gabata.

Ya ce, ba shakka kiran yazama wajibi idan aka yi la’akari da yadda a yanzu maimakon rungumar zaman lafiya da hadin kan al’umma bayan zaɓukan a jihar sai wasu cikin ’yan siyasan suna ta zargin mutane da wasu addinai cewa ba su zaɓe su ba da sauran su. 

Ya ƙara da cewa, yakamata da waɗanda suka yi nasara a zaɓukan da waɗanda ba su yi ba duk su mance da abubuwa da suka faru kafin lokaci da kuma bayan zaɓukan su riƙa tunanin cigaban jihar da ƙasa maimakon haka.

Shugaban ƙungiyar CAN ɗin na jihar Nasarawa dokta Sunday Emmah ya kuma ƙalubalanci ’yan siyasa su yi amfani da bambance-bambance da ra’ayoyi daban-daban da aka gano a lokutan zaɓukan wajen haɗa kawunan al’umma da tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna don kada haka ya sake faru nan gaba.

Dangane da dangantakar da ke tsakanin ƙungiyar sa ta CAN da takwarar ta ta Musulmi wato J.N.I a turance a jihar, Emmah ya bayyana cewa, kawo yanzu suna aiki tare kuma babu wani rashin jituwa tsakanin ƙungiyoyin addinan biyu a jihar.

Ya kuma yi amfani da damar inda ya musanta wani jita-jita da wasu ke cigaba da yaɗa a jihar cewa akwai rashin jituwa da gaba tsakanin ƙungiyoyin 2 a jihar inda ya buƙaci al’umma suyi wasi da jita-jitar.

Kawo yanzu dai binciken wakilin mu ya gano cewa bayan an kammala zaɓukan na 2023 a jihar wasu ’yan siyasa musamman waɗanda suka yi nasarar lashe zaɓukan da ƙyar na cigaba da zargin wasu al’umma da ƙungiyoyin addinai cewa basu zaɓe su ba kuma ba za su yi musu aiki ba saboda haka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *