Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin ƙasar Canada ta sanar da soke katin biza mai wa’adin shekara goma ga ƴaƴan Nijeriya da na wasu ƙasashe.
Hukumomin ƙasar sun ce hakan ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatin wajen rage adadin shige-da-fice tun bayan aukuwar annobar COVID-19.
Bizar, wadda ta ke bada damar shiga da fita ƙasar a lokacin da mutum ya ke so, an soke amfani da ita ne a matsayin karɓaɓɓiyar shaida.
Da farko dai, ƙasar ta bada damar amfani da biza iri biyu; wadda ke bada damar shiga ƙasar a kodayaushe da kuma wacce ke sa a shiga bisa wani dalili na musamman kamar taruka da makarantunsu, inda jama’a da dama suka fi amfani da na farkon.
A sakamakon haka ne hukumar shige-da-fice ta ƙasar za ta yi hukunci game da wa’adi da tsarin biza mai amfani a mataki na musamman la’akari da yanayin matafiya.