Kiraye-kiraye ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu kan ya naɗa shugaban ƙungiyar matasan Arewa (AYCF), Yerima Shettima, a matsayin minista na ci gaba da samun tagomashi inda a yanzu ita ma ƙungiyar Progressive Young Leaders Assembly ta shiga sahun masu wannan ra’ayi.
Shugaban ƙungiyar, Abubakar Kurawa, ya bayyana a cikin sanarwar da ya fitar cewa naɗa Shettima muƙamin minista zai zama shaidar cewar Tinubu zai yi aiki tare da matasa s gwamnatinsa.
A cewar ƙungiyar, “Mun lura da muhawarar da ake tafkawa kan buƙatar Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta bai wa matasa damar riƙe muƙamin minista.
“Mun fahimci Shugaban ya samar da tsari na musamman wajen raba muƙaman siyasa wanda ya shafi fito da zaƙaƙuran matasa masu kishin ƙasa.
“Da wannan dalili ne mu ma muka shiga sahun masu kira ga Shugaba Tinubu kan ya duba sannan ya naɗa Alhaji Yerima Shettima na a AYCF a matsayin minista a gurbin Jihar Kaduna,” in ji ƙungiyar.
Ƙungiyar ta ƙara da cewa, Alhaji Shettima ya kasance mai son cigaban tattalin arzikin matasa domin rage aikata manyan laifuka a tsakanin matasa.