
Daga BELLO A. BABAJI
CANEX 2024 wani gagarumin taro ne da za a gudanar da bikin al’adun Afirka acikin sa inda za a yi wasanni da harkokin nishaɗi wanda na wannan shekarar a ranar 16 ga watan Oktoba za a gudanar da shi.
A yayin taron, manyan mutane da taurari da jaruman finafinai za su gabatar da jawabi waɗanda akwai Ministar Al’adu ta Nijeriya, Hannatu Musa Musawa da jarumin finafinan Hausa kuma Darakta-Manaja na Hukumar Finafinai ta Ƙasa, Dakta Ali Nuhu.
Taron zai kuma nuna yadda Nijeriya ke da al’adu masu ƙarfi inda za a samu wakilai a ɓangarorin waƙa, da rawa da wasu nau’ukan al’adu daban-daban.
Haka nan, akwai shahararren mawaƙin nan na Nijeriya mai suna Qing Madi wanda zai gabatar da waƙa ta kai-tsaye.
Sannan Chef Stone, wanda ƙwararre ne a harkar dafa abinci, zai shiga sahun waɗanda za su baje kolin girke-girke.
Har’ilayau, taron zai ƙunshi wasannin kala-kala duk don nuna yadda al’adun ƴan Afirka da kuma ci-gaba a ɓangarori daban-daban da suka shafe su da yankin ke samu.