Canjin kuɗi: APC ta buƙaci Emefiele da Malami su yi murabus saboda ɗora Buhari kan bauɗaɗɗiyar hanya

Daga BASHIR ISAH

Shugabancin Jam’iyyar APC a shiyyar Arewa maso Yamma, ya buƙaci Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele da Babban Lauyan Ƙasa, Abubakar Malami, da su ajiye aikinsu.

APC ta buƙaci hakan ne saboda zargin su biyun da ɗora Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari kan bauɗaɗɗiyar hanya dangane da sabon tsarin nan taƙaita ta’ammali da tsabar kuɗi, wato “cashless policy”.

A ranar Juma’a Kotun Ƙoli ta yanke hukuncin ci gaba da amfani da tsoffin N200, N500 da N1000 zuwa Disamban 2023 biyo bayan ƙarar da wasu gwamnonin APC uku suka shigar kan Gwamnatin Tarayya.

Gwamnonin da lamarin ya shafa sun haɗa da Nasir El-rufai (Kaduna) da Bello Matawalle (Zamfara) da kuma Yahaya Bello (Kogi), sun maka gwamnatin a kotu ne don nuna rashin yarda da wa’adin daina amfani da tsoffin kuɗi da gwamatin ta ƙayyade.

Cikin sanarwar da ya fitar a Abuja ran Juma’a kan hukuncin da Kotun Ƙolin ta yanke, mataimakin shugaban APC na ƙasa a shiyyar Arewa maso Yamma, Malam Salihu Moh Lukman, ya ce, “Abin takaici ɗora Shugaba Muhammadu Buhari a kan bauɗaɗɗiyar hanya wajen aikata abin da ya saɓa ma doka kamar yadda Kotun Ƙoli ta bayyana.

“Mu da sauran ‘yan Nijeriya muna godiya ga Alƙalan Kotun Ƙolin ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Akomaye bisa wannan hukunci…”

Ya ce wajibi ne Emefiele da Malami su girbi abin da suka shuka wajen kitsa al’amarin canjin kuɗi kasancewarsu masu riƙe da muƙaman gwamnati.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *