Canjin kuɗi: Gwamnoni sun bai wa Malami, Emiefele wa’adin biyayya ga umarnin kotu

Daga BASHIR ISAH

Gwamnonin da suka maka Gwamnatin Tarayya a kotu kan batun canjin kuɗi sun bai wa Babban Lauyan Ƙasa kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, SAN, tare da Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, zuwa ranar Talata kan su yi wa umarnin Kotun Ƙoli biyayya.

Gwamnonin na buƙatar Gwamnati da CBN su mutunta umarnin kotu wajen tsawaita wa’adin tsoffin takardun kuɗi na N200, N500 da N1,000 zuwa 31 ga Disamban 2023 kamar yadda kotun ta buƙata.

Gwamnonin sun yi barazanar shigar da ƙara kotu a kan Malami da Emefiele muddin aka wuce ranar Talata ba tare da sun yi wa umarnin na kotu biyayya ba.

Idan za a iya tunawa Manhaja ta rawaito yadda a ranar 3 ga Maris Kotun Ƙoli ta yanke hukunci kan ci gaba da amfani da tsoffin N200 da N500 da N1,000 har zuwa ƙarshen wannan shekara da ake ciki.

Sai dai rahotanni sun nuna a ƙalla wasu gwamnoni su 10 sun kimtsa don maka Gwamnatin Tarayya da CBN a kotu saboda ƙin kiyaye umarnin kotun.

Gwamnonin da lamarin ya shafa kamar yadda rahotannin suka nuna, sun haɗa da gwamnonin Kaduna, Kogi, Zamfara, Ondo, Ekiti, Katsina, Ogun, Cross River, Legas da Sakkwato, waɗanda aka ce a Juma’ar da ta gabata suka tunatar da Malami hukuncin tsawaita wa’adin tsofaffin kuɗin da kotu ta yanke.

Babban Lauyan Jihar Zamfara kuma Kwamishinan Shara’a na jihar, Junaidu Aminu, ya faɗa a ranar Lahadi cewar tun da Gwamnati ta ƙi aiwatar da umarnin na kotu, masu ƙara na damar sake garzayawa Kotun Ƙolin don tabbatar da an yi abin da ya dace.