Canjin kuɗi: Majalisar Dattawa da EFCC sun bayyana matsayarsu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Majalisar Dattawan Nijeriya ta ce, wa’adin ranar Talata 31 ga Junairu, 2023 da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayar na canja dukkan tsoffin kuɗaɗe zuwa sabbi a bankuna, ya yi kaɗan.

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da majalisar ta yi alƙawarin bayar da goyon bayan majalisa ga manufar CBN na sake fasalin Naira.

Ƙudurin majalisar ya biyo bayan ƙudirin da Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Banki, Inshora da sauran Cibiyoyin Hada-hadar Kuɗi, Sanata Sani Uba ya gabatar a ranar Laraba 16 ga watan Nuwamba, 2022.

Majalisar Dattijai ta yi kira ga babban bankin CBN da ya wayar da kan jama’a musamman a yankunan karkara domin ganin an wayar da kan ’yan Nijeriya kan wannan sabuwar manufa.

’Yan majalisar sun dage cewa irin wannan wayar da kan jama’a zai taimaka wa ’yan Nijeriya mazauna yankunan karkara wajen bin wannan manufa ta yadda ba za su yi asarar kuɗaɗen shiga da suke samu ba.

Idan dai za a iya tunawa, a watan Oktoba ne gwamnan babban bankin ƙasar CBN, Godwin Emefiele ya bayyana shirin sake fasalin takardun kuɗi na naira 200, 500, da 1000.

Emefiele ya ce, abin damuwa ne yadda aka rasa sanin inda kashi 85 cikin 100 na kuɗaɗen da ke zagawa tsakanin ’yan Najeriya ke shiga.

Ya kuma buƙaci ’yan Nijeriya da su ci gaba da zuwa bankunansu don saka takardun kuɗinsu na Naira, inda ya ƙara da cewa, za a yi watsi da kuɗin ajiya na hada-hadar kaqa da N150,000.

Emefiele ya ƙara da cewa, sake fasalin kuɗin Naira zai taimaka wajen daƙile kuɗaɗen jabu, da kuma kawo cikas ga biyan kuɗin fansa ga ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane.

Majalisar Dattijai a ranar Larabar da ta gabata ta buƙaci babban bankin ƙasar CBN da ya samar da matakai ta fuskar fasahar hada-hadar kuɗi (FinTech) a ko’ina domin tabbatar da cewa al’ummar yankin sun samu damar bankaɗo kudaɗensu cikin sauƙi cikin lokacin da aka ƙayyade.

’Yan majalisar sun ce irin wannan matakin zai kuma tabbatar da tsaron al’ummar yankin da za a iya yi musu ɓarna tare da kwace musu kuɗaɗensu daga hannun masu laifi kamar ’yan bindiga da masu tayar da ƙayar baya.

Yawancin Sanatoci a sassan jam’iyya na goyon bayan sake fasalin kuɗin Naira amma wasunsu na nuna damuwa kan wa’adin da babban bankin ya sanya na ajiye tsofaffin takardun kuɗi a bankunan kasuwanci.

Kwanaki biyu da suka gabata ne CBN ya ce, ya yi tanadi ga ’yan Nijeriya mazauna karkara domin musanya musu takardun kuɗi na Naira yayin da bankin ke yunƙurin sake fasalin takardun kuɗi 200, 500 da 1000.

Babban bankin na CBN ya dage cewa matakin zai taimaka wajen duba hauhawar farashin kayayyaki, jabun da kuma adadin kuɗaɗen da ba na tsarin banki ba.

A ɓangare guda kuma, Shugaban Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya ce, dala za ta iya faɗuwa zuwa Naira 200 bayan sake fasalin Naira.

Bawa ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da Sashen Hausa na Deutsche Welle (DW), inda ya ce, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya amince wa sake fasalin.

Idan dai za a iya tunawa, bayan da babban bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana shirin sake fasalin kuɗin ƙasar, Naira, sai ga kuɗin ƙasar ya fuskanci matsin lamba sosai a kasuwar bayan fage.

Sai dai a ranar Litinin ɗin da ta gabata ne kuɗin ya fara koma baya a kan koma bayan tattalin arziki, bayan da jami’an hukumar EFCC suka matsa lamba kan dillalan canjin kuɗaɗen ƙetare a Abuja da Legas da Kano da sauran manyan biranen ƙasar na tsawon mako guda.

An ce, matsa lambar da aka yi wa dillalan kuɗaɗen ya tilastawa wasu BDC ɗin voye kuɗaɗe, matakin da aka ce ya sanya wasu da dama da aka fallasa a siyasance da masu hasashen kuɗin suka ja da baya kan buƙatarsu ta neman ƙazamin riba.

Rahotanni sun bayyana cewa, Naira ta samu kashi 20.8 bisa dala bayan da ta yi asarar kashi 36.52 na darajarta a kusan watanni 11 a kasuwar hada-hadar.

Da ya ke magana a cikin hirar, Bawa ya ce, ƙoƙarin EFCC zai ɗore kuma yana kyautata zaton Naira 200 za ta saya Dala 1.

Shugaban hukumar ta EFCC ya kuma ce babu wata manufa ta siyasa a bayan wannan ra’ayin, ta kuma yi kira ga ’yan Nijeriya da su kai rahoton duk wanda ya ke da kuɗaɗen da aka karɓa.

A cigaba da batun dai, Shugaban Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC), Abdulrasheed Bawa, a ranar Alhamis ya ce, adadin gwamnonin da suka ƙirƙiro da sabon salon tara kuɗaɗe gabanin canja fasalin Naira ya ƙaru.

Bawa ya bayyana hakan ne yayin da ya ke zantawa da manema labarai a fadar shugaban ƙasa bayan ganawa da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 17 ga watan Nuwamba 2022.

Idan dai za a iya tunawa, bayan da babban bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana shirin sake fasalin kuɗin ƙasar na Naira, sai ga kuɗin ƙasar ya fuskanci matsin lamba sosai a kasuwar bayan fage.

Sai dai a ranar Litinin da ta gabata ne kuɗin ya fara koma baya a kan koma bayan tattalin arziki, bayan da jami’an hukumar EFCC suka fara matsala lamba kan dillalan canjin kuɗaɗe a Abuja da Legas da Kano da sauran manyan biranen ƙasar hari na tsawon mako guda.

Bawa, wanda ya ƙi bayyana adadin gwamnonin da ke ƙarƙashin hukumar EFCC, ya kuma qi bayyana sunayen gwamnonin.

Shugaban na EFCC ya ci gaba da tabbatar da cewa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta gamsu da sake fasalin takardar kuɗin Naira, inda ya bayyana cewa, manufar za ta taimaka wa babban bankin Nijeriya (CBN) wajen sarrafa kuɗaɗen da ke cikin tsarin tare da kara wa mutane damar samun ƙarin kuɗaɗe.

Bawa ya kuma sake bayyana yardarsa a matsayin masanin tattalin arziki cewa, sake fasalin Naira zai sa darajar dala a halin yanzu ta kai 890 ta sauko zuwa Naira 200.

Kan ayyukan da aka yi wa ma’aikatan Ofishin De Change (BDC), ya tabbatar da cewa aikin ya yi nasara kuma an samu canja sosai.

Bawa ya sake yin kira ga ’yan Nijeriya da su rungumi sabuwar manufar, tare da ƙarfafa gwiwar ’yan ƙasar da su yi amfani da wannan tsarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *