Canjin Kuɗi: Matakin taƙaita cire kuɗi ya saɓa wa doka – in ji Kotun Ƙoli

Daga BASHIR ISAH

Kotun Ƙoli ta yanke hukuncin cewar matakin taƙaita cire kuɗi da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ɗauka wanda hakan ya haifar da karancin kuɗi a ƙasa, hakan ya saɓa wa dokar ‘yancin ‘yan ƙasa.

Kwamitin alƙalan ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a John Okoro, ne ya bayyan wannan hukuncin yayin zaman Kotun ranar Juma’a.

“Irin wannan ƙayyadewar a kan ‘yancin da mutum ke da shi na yin amfani da dukiyarsa yadda ya so saɓa wa doka ne, sai dai idan doka ce da kanta ta tanadi hakan,” in ji ɗaya daga cikin alƙalan, Emmanuel Agim.

Yayin zaman nata, Kotun ta yi matsayar a ci gaba da amfani da tsoffin N200 da N500 da kuma N1,000 har zuwa ƙarshen wannan shekarar.

A matsayin ɓangare na sabbin dokokin hada-hadar kuɗi da ta samar, Gwamnatin Tarayya ta sauya fasalin N200 da N500 da N1,000 a watan Oktoban 2022, kana ta yi nufin daƙile tsoffin kuɗin da sauyin ya shafa cikin kwana 90.

Kazalika, daga cikin sabbin dokokin har da taƙaita cire kuɗi a banki da CBN ya yi zuwa N500,000 a mako ga ɗaiɗaikun jama’a, sannan Naira miliyan 5 ga hukumomi da ma’aikatu a mako guda.

Sai dai aiwatar da sabbin dokokin ya haifar da ruɗani a ƙasa, inda ƙarancin sabbin kuɗin ya haifar da rashin kuɗi a hannu mutane.