Canjin takardun Naira: Kakakin Majalisa ya yi barazanar cafko masa Emefiele

•Yadda al’amura suka kwaɓe

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila, ya ce, zai bayar da umarnin a cafko masa Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, da manajan daraktocin bankuna bisa kunnen uwar shegu kan sammacin da majalisar ta aika musu kan batun canjin sababbin takardun kuɗi.

Kakakin Majalisar ya bayyana hakan a zauren majalisar jiya Alhamis, 26 ga Janairu, 2023, yana mai cewa, maimakon majalisar ta ɗage zamanta zuwa ranar 28 ga Fabrairu, 2023, bayan kammala zaven Shugaban Ƙasa da na Majalisar Dokoki ta Ƙasa, kamar yadda tun da fari aka tsara, yanzu za ta sake zama a ranar Talata mai zuwa, don ɗaukar mataki kan Emefieli da shugabannin bankuna da suka gaza gurfana a gaban majalisar.

A ranar Talatar da ta gabata dai Majalisar wakilai ta kafa kwamiti na musamman ƙarƙashin jagorancin Shugaban Masu Rinjaye, Alhassan Ado Doguwa, don ganawa da Gwamnan CBN da shugabannin bankunan Nijeriya kan wa’adin daina amfani da tsofaffin takardun kuɗin, inda aka tsara ganawar a ranar Laraba, amma sai Bankin CBN ya buƙaci a ɗage zaman zuwa jiya Alhamis, saboda an kai musu takardar gayyatar a ƙurarren lokaci. To, amma a zaman majalisar na jiya, sai Hon. Doguwa ya sanar da Babban Zauren Majalisar takaicinsa na yadda waɗanda aka gayyata ɗin suka ƙi halartar zaman kwamitin.

“Gwamnan CBN bai zo wajen ba, kuma babu wanda ya zo a madadinsa,” inji shi, yana mai ƙarawa da, “ga waɗanda suke ta faman nacewa akan tsarin ba gudu ba ja da baya, ya kamata su san cewa, wannan manufa ce ta gwamnati kawai, amma ba dokar ƙasa ba. Duk lokacin da ka zo da manufa ko tsari na gwamnati, wanda ba zai aikatu ba, daidai ne majalisa ta ɗauki mataki.”

Daga nan sai Gbajabiamila ya karanta takardar da Emefiele ya aiko wa majalisar mai ɗauke da sa hannun Mataimakin Gwamnan CBN, yana mai sanar da cewa, ba Gwamnan na CBN ba za samu halartar zaman kwamitin ba, saboda yana cikin tawagar wakilan Shugaban Ƙasa dake Ƙasar Senegal. Don haka a yayin da ya ke nuna ɓacin ransa kan wasiƙar, Gbajabiamila ya ce, ba amincewa ba ne kan yadda Gwamnan CBN ya yi kunnen uwar shegu da gayyatar Majalisar Wakilai.

“Majalisar Wakilai ta ɗauki mataki kan qudiri game da wani abu wanda ya shafi al’umma da ya sanya ta gayyaci Gwamnan Babban Bankin Nijeriya da manajan daraktocin bankuna a Nijeriya su bayyana a gaban Majalisar Wakilai,” inji shi, yana mai ƙarawa da cewa, “an an gayyace su ne don su bayar da dalilan da suka sa aka kasa samar da isassun sababbin takardun kuɗi kafin ranar qarewar wa’adin da tsofaffin kuɗin za su daina aiki daga 31 ga Janairu, 2023.

“Majalisa ta kafa kwamitin musamman a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Masu Rinjaye, Alhassan Ado Doguwa, don wannan dalilin. Babu ko ɗaya daga cikin shugabannin bankunan da suka halarci zaman ko bayar da isasssun hujjojin kasa amsa sammacin Majalisar Wakilai ba.

“Wannan ba abin amincewa ba ne. Ƙudirin da Majalisa ta amince da shi ya nuna cewa, an gaza wajen samar da isassun sababbin takardun kuɗin. Wannan gazawar tana da matuƙar tasiri mummuna kan ’yan Nijeriya da harkokin kasuwancui da sana’o’insu a faɗin ƙasar. Ƙin amsa gayyatar Majalisar Wakilai kan batun ya nuna yadda bankunan ba su mutunta walwalar ’yan Nijeriya, waɗanda su ne kwastomominsu. Kuma cin zarafi ne ga Majalisar Dokokin Ƙasa.

“Don haka, idan har daga yanzu zuwa ƙarshen yau (Alhamis) aka cigaba da samun turjiya kan amsa sammacin Majalisar Wakilai, ba tare da vata lokaci ba, bisa la’akari da ikon da dokar ƙasa ta bayar a Sashe na 89 (1) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya da Sashe na 19 (2) (1) na Dokar Majalisar Wakilai, ba zan yi ko ɗar ba wajen umartar Sufeto Janar na ’Yan Sandan Nijeriya da ya tilasta wa Bankin CBN ko manajan daraktoci, waɗanda suka ƙi, gaza ko wasarairai da gurfana a gaban Majaisar Wakilai ba.”

Daga nan sai Kakakin Majalisar Wakilan ya yi ƙarin haske da cewa, Majalisar ta amince da ikon Bankin CBN na sauya fasalin Naira bisa amincewar Shugaban Nijeriya, amma hakan ba ya nufin ta yi wasarairai da rayuka ko buƙatun ’yan qasa ba, waɗanda suka a’ala!

Yadda al’amura suka kwaɓe

Daga SANI AHMAD GIWA da MOHAMMED AL-AMEEN

Al’ummar Nijeriya sun shiga fargaba dangane da wa’adin da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ƙayyade na ranar 31 ga Janairun 2023 da za a daina karɓar tsoffin takardun Naira a faɗin ƙasar.

Lamarin da ya haddasa gagarumin cunkuso a rassan bankunan ƙasar, kana ya saka fargaba a zukatan ‘yan kasuwa musamman masu shaguna da sauran masu hada-hadar kuɗi na yau da kullum, inda da yawan ‘yan kasuwa da masu ƙananan sana’o’i suka daina karɓar tsoffin takardun N200 da N500 da kuma N1000 tare da garƙame shagunansu don guje wa yin asara duba da ƙaratowar lokacin da CBN ya ƙayyade.

Hakan ne ya sa ‘yan Nijeriya suke ta yin karaye-kiraye ga Gwamnan CBN da gwamnatin ƙasar da ta tsawaita wa’adin amfani da tsoffin takardun Nairar domin su samu damar vatar da su, sai dai Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Mista Godwill Emeifele ya ja daga ya ce babu gudu ba ja da baya, ainihin wa’adin da aka saka ba zai ƙara ko da kwana guda ba a kai, duk da Majalisar Dattawan Nijeriya ta sake umartar CBN da ya aka ƙara wa’adin daina amfani da tsoffin takardun Naira zuwa 31 ga Yuli, 2023, idan ba haka ba ƙasar ka iya shiga ruɗani, a cewar majalisar.

Wannan al’amari dai ya tsoma ‘yan Nijeriya da yawa cikin ruɗani, inda al’ummar jihohin Borno da Yobe suka ce al’amarin yana yi wa tattalin arzikin su mummunan barazanar karyewa, sun ƙara da cewa, hakan yana zuwa ne sakamakon qin tura isassun sabbin kuɗaɗen a bankuna a lokacin da wa’adin yake gabatowa. 

Jama’a da dama a yankin sun bayyana fargabar abubuwan da canjin kuɗin zai iya jawowa. Sun nuna matakin canja tsoffin kuɗin a matsayin wanda ba a yi tunani ba kafin aiwatar da shi, musamman ta hanyar ƙin la’akari da jihohin Bornon da Yobe, waɗanda suka sha fama da ƙalubalen tsaro, wanda hakan ya jawo rufe rassan bankuna da dama a jihohin. 

“Idan za a iya tunawa, Jihar Borno ta na da ƙananan hukumomi 27, kuma kafin matsalar tsaron, akwai rassan bankuna a mafi yawan ƙananan hukumomin; amma yanzu ƙananan hukumomi huɗu ne kacal ake ba bankuna a faɗin jihar Borno, su ne Maiduguri, Jere, Biu da Kwaya-kusur. A Jihar Yobe kuma, daga cikin qananan hukumomi 17, huɗu ne kawai suke da rassan bankuna; Damaturu, Potiskum, Gashu’a da Nguru.”  

Blueprint Manhaja ta zanta da jama’a kan wannan batun, yayin da Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Kasuwa a Ƙaramar Hukumar Potiskum, kuma cibiyar kasuwanci a jihar Yobe, Alhaji Nasiru Mato ya ce, “Wannan mataki ya yi tsauri sosai ga talaka, inda harkoki suka tsaya cak saboda yadda babu sabbin kuɗin kuma wasu ‘yan kasuwa sun dakatar da karvar tsoffin kuɗin, don kauce wa asara.

“Sannan a yanayin Jihar Yobe, shi ne muna fuskantar ƙarancin bankuna kuma ba a kawo sabbin kuɗin ba, ka ga kenan hakan zai shafi tattalin arzikinmu. Kuma mafi yawan al’ummar mu mazauna ƙauyuka ne, idan manomi ko talaka ya na kawo kayan gona ko dabbarsa domin ya sayar ya yi cefane ne kawai, kuma ba kowa ne yake da asusun banki ba a qauye. Kuma ina bankunan suke a nan Yobe?

“Bisa ga ƙiyasin da mu ka yi, kowane mako ana hada-hadar kasuwancin sama da Naira biliyan biyu a garin Potiskum; saboda yadda muke da manyan kasuwanni; kasuwar dabbobi da ta kayan abinci. Waɗanda kuma ake zuwa ci daga kusan kowane ɓangarorin ƙasar nan da wasu ƙasashen waje. Muna da manyan motocin dakon kaya kusan suna zuwa kowane lungu da saƙon ƙasar nan. Kuma ga wannan halin da aka jefa mu na canjin kuɗi, wanda ba a yi tunani ba kafin a aiwatar da shi ba,” inji shi. 

Shi ma da yake tofa albarkacin bakin shi, Shugaban ƙungiyar ‘yan kasuwar jihar Yobe, Alhaji Usman Mu’azu, ya bayyana fatansu ga Gwamnatin Tarayya wajen duba halin da jama’a suke ciki tare da roƙon ƙara lokacin, inda ya ce, “a makonnin da suka gabata, jami’an Babban Bankin Nijeriya (CBN) dake nan Damaturu sun tara mu domin faɗakar da mu kan matakin canjin tsoffin kuɗin, wanda daga bisani muka sanar da shugabannin ‘yan kasuwa a ƙananan hukumomi.

“Sannan mun buqaci su taimaka mana wajen ƙara lokacin wa’adin canja tsoffin kuɗin, amma sun nuna mana abu ne mai kamar wuya.”

Ya ce sakamakon mawuyacin halin da ake ciki, harkokin kasuwanci sun yi ƙasa sosai, kuma hakan zai shafi tattalin arziki da Jihar Yobe baki ɗaya. 

Wani ɗan kasuwa a birnin Maiduguri, Alhaji Usman Abubakar, ya ce, “wa’adin canjin tsoffin kuɗin ya ɗaure wa mutane kai, musamman mu ‘yan kasuwa; shin idan ka daina karvar tsoffin kuɗin to dame za ka gudanar da kasuwancin, saboda sabbin kuɗin ba su wadata ba.

Saboda ni ɗin nan da nake magana da kai yanzu, a matsayina na ɗan kasuwa, sau biyu ko sau uku na tava ganin sabuwar dubu ɗaya, amma da idona ban tava ganin sabuwar Naira 500 ba, balle kuma 200. Saboda haka mu wannan al’amarin ya ɗaure mana kai, abin nan fa za a yi haihuwar guzuma; ɗa kwance uwa kwance. Da talakwa da suke zuwa sayen kayan da mu ‘yan kasuwar da ita gwamnatin kanta duk wannan hasarar za ta shafemu.

“Sannan kuma, ko dai gwamnati ta ɗaga wannan wa’adin ko kuma ta koma jami’an gwamnati su zauna su nutsu domin sake nazartar yadda tsarin zai yuwu, ko kuma ta shafi kowa.” 

A nashi ra’ayin, Dr. Babayo Liman, a zantawarsa da ‘yan jarida a birnin Maiduguri, ya ce, “ya kamata gwamnati ta kalli wannan al’amarin da idon basira tare da sauraron ƙorafin talakawa, a matsayin su na ‘yan ƙasa kuma da la’akari da lokacin dimukuraɗiyya ake ba a lokacin mulkin soja ba. Sannan a baya ma an yi irin wannan canjin kuma iyayenmu sun sha wahala, kuma mafi yawan al’ummar mu mazauna ƙauyuka ne, kuma sabbin kuɗin bai wadata a hannun bankuna ba,” inji shi.

A Jihar Neja kuma, iyayen wata amarya a Ƙaramar Hukumar Gbako su ka qi amincewa da sadakinta da aka biya da tsoffin takardar Naira da dangin mai neman auren ‘yarsu suka biya.

Kafofin yaɗa labarai na yanar gizo sun bayar da rahoton cewa, mutane da dama a ƙauyen na fargabar amsan tsofaffin takardun kuɗi saboda fargabar cewa ba za su iya kashe su ba kafin wa’adin ranar 31 ga watan Janairu da muke ciki.

Rahotanni sun bayyana cewa, dangin mai neman auren sun je biyan sadakin amaryar tare da kuɗin wasu kaya na shirye-shiryen ɗaurin auren kafin daga bisa aka gane sun zo da tsofaffin takardun Naira.

Duk da cewa ba a ɗage ɗaurin auren ba, amma dangin amaryar sun bayyana cewa a ranar 31 ga watan Janairu ne Babban Bankin Qasa CBN ya sa wa’adin daina amfani da tsoffin kuɗi kuma ba su tashi siyan kayayyakin da ake buƙata ba domin bikin, kuma ba su da asusun ajiyar kuɗi a banki, don haka suna buƙatar sabbin takardun kuɗi.

Wani dangin mai neman auren ya bayyana cewa: “Mun kai kuɗin sadaki ga dangin yarinyar da muke son aura. Sun kira ni ranar Lahadi don in zo in mayar da tsofaffin takardun kuɗin kafin lokacin da muke da sabbin takardun Naira. Sun ce ba su da inda za su canza tsoffin kuɗin. Don haka, Ina so in kai su banki har zuwa lokacin da muka samu sabbin takardun kuɗin.”

Jama’a da dama na fargabar karɓar tsofaffin takardun kuɗin ne saboda fargabar cewa ba za su iya kashe su ba kafin wa’adin ranar 31 ga watan Janairu da Babban Bankin Nijeriya CBN ya ƙayyade lokacin da tsofaffin takardun Naira za a daina amfani da su ba.